Blog Archive

Tuesday 22 August 2017

SIHIRI: RIKICI YA BARKE A FADAR PDP

RIKICI YA BARKE TSAKANIN SHUGABANIN PDP DA BOKAYEN DA SUKA GAYYATO DAGA KASAR INDIYA. Rahotanin daga ofishin jam'iyar PDP da ke Abuja, na nuni da cewa ana can ana dauki ba dadi tsakanin shugabanin PDP da Allolin su. Watau mashahuran bokayen nan da suka gayyato daga kasar Indiya domin halaka shugaba Buhari. Takardamar ta samo asali ne tun satin da ya gabata lokacin da wasu gwamnoni suka kai wa shugaba Buhari ziyara a London, inda ta bayyana cewa Buhari ya sami lafiya sabanin alkawalin da bokayen sukayi na cewa da gawar Buhari za' a dawo a Najeriya. Ganin Buhari ya sami lafiya sai daya daga cikin shugabanin PDP tsohon gwamnar wata jaha dake mukwabtaka da Jahar Kebbi da Zamfara ya kira taron gaggawa, inda suka gayyaci shugaban matsafan mai suna Mugulor Prasad da wakilin sa a Najeriya Guru Muhraj, inda shugabanin PDP suka nuna bacin ransu akan kasa halaka Buhari, suka kuma zargi Guru Mahraj da cin amana saboda ya fito kafafen yada labarai yanayi wa Buhari tayin cewa zai iya warkar da shi bayan PDP ta bashi Naira Miliyan 170 (N170 m) domin sihirce Buhari. A wancan taron gaggawan ne Boka Mugulor Prasad na kasar Indiya ya nemi da akara masa kudi dola miliyan 40 ($40m) bayan dola miliyan 60($60m) da aka bashi kafin ya yarda yazo Najeriya kuma kai tsaye aka bashi wadannan kudaden. Lamarin ya cabe ne a ranar Asabar 19/8/2017 bayan Shugaba Buhari ya dawo lafiya a raye, sai shugabanin PDP suka nemi boka Mugulor da Guru Mahraj da su mayar masu da kudaden su tunda sun kasa halaka Buhari. Bukatar da bokayen sukayi watsi da ita suka kuma kalubalanci shugabanin PDP da cewa sukai karan su a kotu idan suna bukartar kudaden su. A ranar Lahadi 20/8/2017 boka Mugulor da tawagar sa suka fice daga Najeriya inda suka bi jirgin Ethiopian Air Line domin komawa kasar su ta INDIYA yayin da shi kuma Guru Mahraj ya fice zuwa matsafarsa da ke dajin garin Ibadan. Yanzu PDP ta zama babu tsuntsu babu tarko; basu ga Allah basu ga Annabi, babu kudi babu mulki. Duk sihirin da suka shekaro sunayi wa Buhari Allah ya juya shi zuwa Vitamin 'A' a jikin Buhari la'akari da kwarin da wannan datijjo ya dawo a cikin sa. Ko wayannan shugabanin PDP za su shigar da kara kamar yadda bokayen suka kalubalance su, ko hasara zasu runguma kamar yadda ta zama sana' a a gare su? Lokaci zai nuna. Daga Amb Abu bako

No comments:

Post a Comment

My credentials still with military, Buhari tells INEC

Over 70 out of the 91 political parties are presenting presidential candidates that will participate in the 2019 Presidential elections...