Blog Archive

Tuesday 22 August 2017

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya kuma koma aiki, inda suke bayyana abinda suka fi so shugaban ya fi mayar da hankali a kai.
Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ga ‘yan kasar mutane da dama suke ta bayyana ra'ayinsu kan abinda ya kamata ya fuskanta. A irin muhawarorin da ake ta yi, wasu sun bayyana ra’ayinsu kan abubuwan da shugaban ya kamata ya fuskanta da suka hada da tunkarar matsalar tsaro da kuma yajin aikin da malaman jami’a ke yi. ‘Yan Najeriya da dama na da ra’ayin cewa tun bayan tafiyar Buhari jinya, harkar tsaro ta tabarbare musamman game da batun Boko Haram da kuma yawaitar satar mutane domin neman kudin fansa. Ba ma ‘yan Najeriya kadai ba, a kasashe makwabta irinsu Jamhuriyar Nijar, jama’a da dama sun yi kira ga shugaban da ya tunkari matsalar tsaro musamman ta Boko Haram, lura da cewa wannan matsala ta shafi kasarsu. Shugaba Buhari ya dawo Najeriya ne a ranar Asabar bayan da ya kwashe sama da watannin uku yana jinya a London kan cutar da har yanzu ba a bayyana ba. Tun a farkon watan Mayu, Buhari ya tafi London, lamarin da ya sa wasu masu fafituka suka yi ta korafin cewa ya kamata ya dawo ko kuma ya sauka a mulki.

No comments:

Post a Comment

My credentials still with military, Buhari tells INEC

Over 70 out of the 91 political parties are presenting presidential candidates that will participate in the 2019 Presidential elections...