Thursday, 24 August 2017
Darikar Tijjaniya Na Ziyarar Wayar da Kawunan Jama'a kan Gujewa Ta'addanci
Saboda yadda wasu ke fakewa da addini suna kafa kungiyoyin ta'addanci ya sa shugabannin darikar Tijjani soma kai ziyara jihohin Najeriya inda yanzu suna jihar Neja domin jawo hankalin mutane su gujewa shiga ta'addanci da sunan addini.
Shugabannin kungiyar darikar Tijjaniya sun isa jihar Neja a cigaba da rangadin fadakar da al'umma illar shiga kungiyoyin ta'addanci da sunan addinin Musulunci.
Kungiyar tace ziyarar fadakar da jama'a na cikin ayyukan da ta sanya a gaba a daidai wannan lokacin da ake matukar bukatar hadin kan al'umma a matakai daban daban a kasar.
Shaikh Sayyadi Kasimu babban sakataren kungiyar a Najeriya ya yi karin haske akan dalilin ziyararsu zuwa jihar Neja.
Yana mai cewa sun isa jihar ne a karkashin jagorancin Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da kuma sunan shugaban darikar na kasa Shaikh Tijjani Ibrahim. Manufar ziyarar ita ce kara dankon zumunci tsakaninsu da 'yanuwansu dake jihar, musamman 'yan darikar Tijjaniya da sauran Musulmai da ma jama'a gaba daya domin samun masalaha.
Inji Shaikh Kasumu suna fadawa 'yanuwa su kara hada kai saboda kasar na bukatar hadin kai wajen yaki da ta'addanci. Sun ba da shawarwari saboda ta'addanci ba addinin musulunci ba ne.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
My credentials still with military, Buhari tells INEC
Over 70 out of the 91 political parties are presenting presidential candidates that will participate in the 2019 Presidential elections...
-
To 'yan'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Mal...
No comments:
Post a Comment